Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki da PDP kan gazawar da suka yi a bangaren mulki tsawon shekaru.

Obi ya yi tsokaci kan gazawar jam’iyyun siyasar biyu ne wajen gyara wutar lantarki bayan shafe shekaru 24 a kan karagar mulki.

Mista Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin kai tsaye.

Dan takarar  ya bayyana yadda jam’iyyun PDP da APC suka yi abin kunya, inda ya ce har yanzu wutar lantarkin Najeriya ba ta tashi daga 4,000 zuwa 5,000 a cikin shekaru 24 da suka gabata ba.

Kafin wannan batu na Peter Obi, a baya ya bayyana cewa, gwamnatin PDP da APC sun ci bashin dala miliyan dubu dari 500 a cikin shekaru 20 na mulkinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *