Babu wata doka da ta hana ni zama kakakin yakin neman zaben APC – Keyamo

Karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi Festus Keyamo, ya ce bai saba wa kowace doka ba, ta hanyar amincewa da zama kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).


Bayan an nada shi a matsayin kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, kungiyar Transition Monitoring Group (TMG), ta bukaci Keyamo ya yi murabus daga mukaminsa na minista.


Sai dai a wata sanarwa da ministan ya fitar, ya ce jam’iyyun adawa ne ke daukar nauyin kungiyar farar hula (CSO).

Ministan ya kuma ce adawa da nadin da aka yi masa a matsayin kakakin jam’iyyar na hana shi hakkinsa.

“Me doka ta ce? Sashi na 84 na dokar zabe ya bayyana karara cewa masu rike da mukaman siyasa za su yi murabus idan za su tsaya takarar kowace jam’iyya ko kuma wani mukami na gwamnati. Ba a bayyana nadin mukamai na wucin gadi na ayyukan jam’iyya ba. Don haka, a zahiri, babu wata doka da ake karyawa a nan,” inji shi.

“Ni cikakken dan jam’iyyata APC ne, kuma na cancanci shiga harkokin jam’iyyar. Duk wata ana cire min kuɗaɗen da na ke ba jam’iyyata daga ɗan ƙaramin albashi da nake samu”.

“Ko motar da nake amfani da ita wajen hira da manema labarai ba motar ma’aikatar ba ce. Tun da na zama minista, ma’aikatar ba ta bani da mota ko ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *