Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin a tura karin jami’an tsaro da a makarantu da asibitocin da ke sassan kasar nan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ta kasa, Olumuyiwa Adejobi, ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Cikin sanarwar, jami’in ya ce an bai wa jami’in ‘yan sanda umarnin su rika sintiri a-kai-a-kai musamman a wuraren da ke fuskantar barazanar tsaro da kuma kai samame irin wuraren don bankado bata-gari.

Babban sufeton ya bayar da umarnin ne bayan ya karbi wasu rahotanni da bayanai daga rundunoni daban-daban na kasar a kan yanayin da al’amuran tsaro ke ciki a kasar.

Babban jami’in dan sandan ya kuma ba wa manyan jami’an ‘yan sanda umarnin su rinka amfani da bayanan sirrin da suka tattara a yayin aikinsu da kuma sanin wadanda ya kamata a tura a wuraren da ke fuskantar barazanar tsaro.

Usman Alkali Baba, ya kuma bukaci al’ummar kasar da su bai wa jami’ansu dukkan goyon bayan da ya kamata a yayin gudanar aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *