‘Yan bindiga sun sace surukar Ango Abdullahi da jikokinsa 4.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da surkuar surukar Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) Farfesa Ango Abdullahi da ’ya’yanta hudu da wasu mata masu danyen goyo.

Maharan sun kai farmaki ne a garin Yakawada da ke Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da surukar dattijon da wasu mutum tara.

Majiyarmu ta ce ’yan bindiga kusan 30 ne suka shiga kauyen da misalin karfe 11 na daren ranar Talata suka je gidan Dakacin Yakawada, Alhaji Rilwanu Saidu da gidan makwabcinsa inda suka dauke mutanen su 10.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin ta wayar tarho, Farfesa Ango, ya ce: “Lallai maharan sun dauke surukata, matar dana, wanda shi ne Sarkin Yakawada da ’ya’yanta guda hudu,” in ji shi.

Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce matar sarkin mai suna Ramatu an sace ta ne tare da ’ya’yanta hudu da suka hada da Rahama da Abdul-azeez da Jidda da wani guda daya.

“Daga nan ne suka shiga gidan makwabcin sarkin, mai suna Abubakar Mijinyawa, inda suka dauke matansa guda biyu, dukkansu da danyen goyo, wato Aisha da Hajara.”

Ya cigaba da cewa, ’yan bindigan sun kuma harbe wani mai suna Aminu Lawal har lahira suka kuam harbi wasu mutum uku, wadanda aka garzaya da su asibiti.

“Wadanda aka harban sun hada da Muhammad Dogari Hakimi da Sama’ila Halliru da kuma Yusuf Aminu.”

Duk kokarinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, abin ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *