Gwamnatin Gombe ta kaddamar da wata rundunar jami’an tsaro
domin yaƙi da matsalar tsaro a jihar.

Gwamnatin Jihar Gombe ta gudanar da taro kan zaman lafiya da lumana, wanda shine taro na farko akan Matsalar Tsaro a Jihar.

Da yaƙe buɗe taron, Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewar taron zai bayar da dama ga jami’an tsaro dana Gwamnati, sauran masu ruwa da tsaki don ganawa da juna tare da tattaunawa kan harkokin tsaro.

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnatin Jihar Ismaila Uba Misilli ya sanya wa hannu aka fitar a ranar Talata.

A lokacin taron, Gwamnatin ta kuma kaddamar da wata Rundunar ta musamman ta tsaro Operation ‘Hattara’ wadda keda nufin ƙarfafa tsaro a Jihar Gombe da kewaye.

Babban mai jawabi a taron Sufeto-Janar na Ƴan sandan Najeriya Usman Baba Alkali ya bayyana cewa taron na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da jami’an ƴan sanda ke ƙoƙarin inganta zumunci a tsakanin Al’umma don magance ta’addanci da sauran ayyuka ashsha.

Leave a Reply

Your email address will not be published.