Sanusi Lamido: “Zan Cigaba Da Magana Kan Matsalolin Najeriya”

Tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi, ya ce zai ci gaba da magana da bayyana ra’ayinsa na kare wa tare da sake gina Najeriya.

Sanusi, wanda shi ne Khalifa na yanzu, na Tijjaniyya, ya bayyana haka ne a Abuja ranar Asabar a wani taro mai taken “Sarki Sanusi: Gaskiya Lokaci Gare Ta.”

Wani farfesa a fannin wasan kwaikwayo a Jami’ar Redeemer Ahmed Yerima ne ya rubuta wasan, kuma shugaban gudanarwa na Duke na Somolu Productions, Mista Joseph Edgar ne ya shirya shi.

Sarkin na 14 ya ce yana da abin da ya kamata ya ba da gudummawar wajen gina kasa saboda dadewar da ya yi a hidimar kasa.

Ya ce ya yi aiki a matsayin Babban Jami’i a Bankin United Bank for Africa, da Bankin First Bank, da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya; a matsayin Sarkin Kano na tsawon shekaru shida da kuma Khalifah, Tijjaniyyat Movement of Nigeria.

Sanusi ya ce ba zai yi godiya ga Allah ba idan ya nuna nadama ko bakin ciki a kan tsige shi daga mukamin sarki duk da mukaman da ya yi a rayuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published.