Keyamo: Aljanna Kadai Ake Samun Cikakken Tsaro, Amma Buhari Ya Yi Iya Kokarin sa.

Keyamo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kare kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na magance rashin tsaro a kasar.

Karamin Ministan Kwadag, Festus Keyamo ya ce a aljanna ne kawai ba za a samu tabarbarewar tsaro ba.

Keyamo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kare kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na magance rashin tsaro a kasar.

A cewarsa, gwamnatin APC ba ta yi alkawarin ba za a yi rashin tsaro ba, amma ta yi alkawarin bayar da isasshen martani wajen magance matsalar rashin tsaro da ake samu a yanzu.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels, Keyamo ya ce: “A Lahira ne kawai ba za a samu tabarbarewar tsaro kwata-kwata ba kuma ba mu isa lahirar ba har yanzu a duniya muke, don haka dole ne a samu matsalar tsaro.

“An taba samun fasa gidan yari a Amurka amma hakan ba yana nufin gwamnati ta gaza ba.

“Ba mu yi alkawarin cewa rashin tsaro ba zai faru ba, mun yi alkawarin mayar da martani; A makon da ya gabata mun kashe wadanda ke cikin daji a Abuja. Yanzu haka dai Abuja tana cikin koshin lafiya, babu wani abin da ya faru a dajin Abuja.

“Mun yi alkawarin mayar da martani kuma mun kai da kyau.

Bai kamata mutane su shiga cikin tashin hankali ba, ‘yan fashi suna son su tsoratar da ‘yan Najeriya ne kawai, iskar oxygen din su ke nan, suna so su haifar da tsoro a tsaanin mu.

“Lokacin da ba ku ba su damar cewa kun tsorata ko firgita ba, sai su tafi

Leave a Reply

Your email address will not be published.