Direkta Janar na NYSC Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Wata ‘Yar Hidimar Kasa Da Ta Rasu.

Babban Darakta Janar na masu yi wa kasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Muhammad Kaku Fadah ya jajantawa iyalan wata ‘yar bautar kasa mai suna Alago Immaculate Chiwendu wanda ta rasu kwanan nan a jihar Bayelsa.

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Eddy Megwa ya sanya wa hannu, marigayiyar, ‘yar asalin Umudim Ngodo Isuochi, karamar hukumar Umunneochie a jihar Abia, ta kasance ma’aikaciyar hidima da aka tura jihar Bayelsa domin bautar kasa na shekara daya.

Da yake jajantawa ‘yan uwan marigayin a gidansu da ke Umuahia, ya bukace su yi addua Allah ya basu ikon jure wannan rashi.

Ya kara da cewa Immaculate ta rasu ne a lokacin da ake bukatar ayyukanta a wani bangare na gudunmawar da take bayarwa wajen ci gaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *