Babbar yaya ga tsohon shugaban ƙasa a lokacin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, Lami Dimka, ta rasu.

Tsohon shugaban ƙasa lokacin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya yi rashin babbar yayarsa mai suna, Maryamu Lami Ɗinka. Marigayya Maryamu, wacce ta kasance yar uwa ɗaya tilo da ta rage wa Janar Gawon a raye, ta mutu ne ranar uku ga watan Agusta a wani Asibitin Jos, babban birnin jihar Filato.

Yar uwar tsohon shugaban ƙasan ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya na tsawon mako shida, babbar ɗiyar mamaciyar, Elizabeth Rimdans, ta tabbatar da mutuwar ga Daily Trust ranar Asabar a Jos.

Elizabeth Rimdans, ta bayyana cewa maharfiyar ta ta rasu ta bar ƴaƴa uƙu, jikoki da dama da ƴaƴak jikoki da yawa.

Haka zalika Misis Elizabeth ta ayyana mutuwar mahaifiyar su da wani babban rashi ga baki ɗaya iyalan gidan su.

Ta ƙara da bayanin cewa: “Ba bu abin da zai maye gurbin raashin mahaifiyar mu, zamu cigsba da rayuwa ne muna tuna ta a kowane lokaci.

Ta kasance mai kirki wacce a ko yaushe take son haɗa kan mutane.

Kafin rasuwarta, marigayya Maryamu ta kasance matar aure ga tsohon kwamishinan yan sanda, Mr S.K. Dimka, kuma mamba da shugaban wasu ƙungiyoyi da dama.

Daga cikin irin waɗan nan ƙungiyoyi akwai Red Cross, ƙungiyar matasan matan kiristoci da ƙungiyar Littafin Kirista Bibul ta Najeriya da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *