Mustapha Balogun, tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), ya rasu.
Majiyar iyalan ta tabbatar da mutuwar Balogun, wanda ya zama IGP a watan Maris na 2002, ga Aminiya a daren ranar Alhamis, amma ba su yi cikakken bayani ba.
An haife shi a ranar 8 ga Agusta, 1947 a Ila-Orangun a Jihar Osun, Tafa Balogun, shi ne Sufeto-Janar na ‘yan sanda na 21.
Ya kasance memba na cadet Assistant Superintendent of Police Course (ASP) Course 3.
Ya yi aiki a jami’an ‘yan sanda daban-daban a fadin tarayya, kuma ya samu karin girma kamar yadda ya kamata, Tafa, ya kasance a lokacin, Principal Staff Officer (PSO) zuwa tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Muhammadu Gambo, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo, tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Delta.
Ya kuma kasance CP a jihohin Ribas da Abia.