Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya tace ta san da yiwuwar ‘Yan ta’adda su aukawa jihar Legas.

Mun samu labari cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Legas suna zaune a cikin shiri bisa zargin hari da ‘yan ta’adda suke shirin kai wa. Daily Trust ta ruwaito cewa Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan reshen jihar, Benjamin Hundeyin, ya fitar da jawabi ya tabbatar da wannan.

A jawabin da SP Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli 2022, ya nuna suna sane da yiwuwar fuskantar wasu hare-haren ta’addanci a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa dakarun jihar Legas sun yi tanadi domin maganin duk wani ko wasu da za su iya kawowa al’umma tashin hankali. Kakakin ‘yan sandan yake cewa babu mamaki ‘yan ta’addan da suka addabi kasar nan suna harin Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published.