An samu tashin hankali a Abeokuta, jihar Ogun, a ranar Lahadi, bayan kama wani da ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa jaridar Aminiya cewa an kama wanda ake zargin shugaban Boko Haram ne a unguwar Ijaye da ke Abeokuta. Majiyar ta ce wanda ake zargin da farko ya yi tirjiya kafin ya mika wuya ga karfin jami’an DSS.
Rahotanni sun bayyana cewa dan ta’addan da ake zargin ya zo Abeokuta ne daga Katsina, inda ya fara aikin tsaro a Ijaye, yayin da yake tattara bayanan sirri kan hare-haren ta’addanci.
Majiyar tsaro ta ce ya koma Abeokuta ne domin ya kafa gungun ‘yan ta’adda domin yin garkuwa da mutane da kuma hare-haren ta’addanci.
Kuma bayan samun bayanan sirri ne jami’an tsaron da ke rike da bindigogi suka kai farmaki maboyarsa suka dauke shi.