Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana fargabar cewa tabarbarewar arziki da talauci idan ba a magance ba, na iya tilastawa wasu ‘yan gudun hijira shiga kungiyar Boko Haram da kungiyar da ta balle – mayakan IS da ke yammacin Afirka (ISWAP).
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a jiya a yayin rufewar sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori-1, Dalori-2, Gubio da Muna da ke Maiduguri, ya ce gwamnatin jihar ba za ta iya ci gaba da ajiye mutanenta a sansanonin ‘yan gudun hijirar ba.
Ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin sa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sake tsugunar da al’umma cikin mutunci.
Zulum ya ce: “Hanya daya tilo da za a magance matsalolin ‘yan tada kayar baya ita ce gwamnati ta magance tushen abin da ya hada da karuwar talauci, karancin ababen more rayuwa da kuma yanayin da ake ciki.