Shugaban Kasa Buhari Ya Bukaci A Tabbatar Da Mai Shari’a Ariwoola A Matsayin CJN.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya (CJN).

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya (CJN).

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar bukatar Buhari kan sake dawowa da zaman majalisar.

Mai shari’a Ariwoola shine mukaddashin alkalan kotunan
Najeriya.

Mai shari’a Ariwoola ya karbi mukamin ne a ranar 27 ga watan Yuni bayan murabus din mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad bisa dalilai na rashin lafiya.

Kafin murabus din mai shari’a Tanko Muhammad, alkalai 14 na kotun koli sun shigar da kara a gabansa bisa zargin rashin kula da jindadin su da kuma karkatar da kudaden kotun koli.

Kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan Adam da al’amuran shari’a na binciken tsohon CJN don tantance sahihancin ko akasin haka na zargin da ke kunshe a cikin karar.

Har ila yau Buhari ya nada wasu daraktoci hudu wadanda ba za su yi aiki ba a babban bankin Najeriya (CBN).

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance wadanda aka nada sannan ta tabbatar da su a matsayin wadanda ba shugabannin CBN ba.

Wadanda aka nada sun hada da: Farfesa Mike Idiahi Obadan ( shiyyar Kudu maso kudu ), Farfesa Odinakachukwu Oniabuko (Kudu maso Gabas), Farfesa Jalingo Mohammed (Arewa maso Gabas) da Adeola Adetunji (Kudu maso Yamma).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *