Yajin aikin ASUU: Ma’aikatan Wutar Lantarki Zasu Shiga Zanga-zangar NLC A Fadin Kasa

Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa za ta bi sahun kungiyar kwadago ta Najeriya NLC domin nuna rashin amincewa da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi.

A cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan Yuli 22, 2022 wanda babban sakataren kungiyar ya fitar, Joe Ajaero ya bukaci daukacin membobin kungiyar da su taka rawar gani a zanga-zangar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne kungiyar NLC ta sanar da fara zanga-zangar hadin gwiwa da sauran kungiyoyin kwadago domin nuna adawa da yajin aikin da ma’aikatan jami’o’in kasar ke yi tun ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

Takardar ta ci gaba da cewa, “Bisa umarnin NLC da matsayar mu da aka bayyana a taron kwamitin tsakiya (CWC) da majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na Majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *