Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan wani faifan bidiyo na ‘yan ta’adda da ke barazanar yin barna a cikin al’umman Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan wani faifan bidiyo na ‘yan ta’adda da ke barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yin barna a cikin al’umman Najeriya, inda ta ce jami’an tsaro suna sane da ‘yan ta’adan kuma suna da hanyoyin yin aikin su da ba za su nuna a kafafen yada labarai ba.

A cikin wata sanarwa da babban mai taimaka shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ya tabbatar wa jama’a cewa shugaban ya yi komai, har ma fiye da yadda ake tunani a matsayinsa na Babban Kwamanda ta hanyar
tallafawa kayan aiki ga sojoji.

Yace suna fatan samun sakamako mai kyau nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *