Gwamnatin Tarraya Zata Kashe Sama Da Naira Biliyan 30 Wajen Gyaran Majalissar Tarayya.

Gwamnatin tarayya ta ce aikin gyaran majalisar dokokin kasar zai lakume Naira biliyan 30.2.

Ministan babban birnin tarayya, Mallam Musa Mohammad Bello, ne ya bayyana hakan a yayin wani rangadin sa ido kan wasu ayyuka da kwamitin majalisar dattijai ya yi a babban birnin tarayya, ranar Alhamis.

An ware Naira Biliyan 37 domin gudanar da aikin gyara a kasafin kudin shekarar 2020 amma an rage shi zuwa Naira Biliyan 9.25 lokacin da aka duba kasafin a tsakiyar shekara.

Sai dai Ministan ya shaida wa kwamitin majalisar dattawa cewa kudin kwangilar aikin ya kai Naira biliyan 30.2 wanda aka biya Naira biliyan 9.2 ga ‘yan kwangilar.

Ya ce kwangilar wadda ta fara a ranar 16 ga Afrilu, 2022, za a kammala ta ne a ranar 15 ga Agusta, 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.