Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da kudin karatu Naira miliyan 5 zuwa ga Musa Sani, wani matashi dan jihar Borno mai shekaru 13, wanda ya yi amfani da laka wajen kwaikwayi gadar sama ta farko da jihar ta yi a zagayen kwastam a Maiduguri.
An biya kudin ne ga Golden Olive Academy da ke Maiduguri domin daukar nauyin karatun Musa tun daga firamare hudu har zuwa kammala babbar Sakandare.
An haifi Musa a unguwar Gwange a cikin Maiduguri. Ya yi makaranta har zuwa firamare uku a makarantar Community a Gwange.
Kwanan nan Musa ya dauki hankalin Zulum lokacin da ya yi amfani da laka wajen kera gadar sama da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a Maiduguri, a watan Disamba.