2023: Peter Obi, Baba-Ahmed sun ziyarci Obasanjo a Abeokuta

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da abokin takararsa, Yusuf Datti Baba-Ahmed, sun ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, a ranar Lahadi.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter tare da raba hotunan taron.

Idan dai za a iya tunawa, a baya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ya ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida a gidansa da ke Minna, babban birnin jihar Neja, domin jin ta bakinsa.

Ziyarar Obi ga tsoffin hafsoshin sojojin biyu na iya zama rashin alaka da samun karbuwa da kuma goyon bayan masu ruwa da tsaki kan burinsu ta hanyar tuntubar juna a fadin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.