Dalilin Da Yasa Ake Kara Kafa Sabbin Jami’o’i a Najeriya – Shugaban TETFUND.

Babban Sakataren Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (Tetfund), Arc Sonny Echono, ya bayyana dalilan da suka sa jami’o’i ke yaduwa a Najeriya, yace haka ya biyo bayan bukatan al’umma.

Echono ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen bukin cika shekaru biyu da kafa Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya, Otukpo (FUHSO) a Jihar Benue.

Ya yi rashin jituwa da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) kan yawaitar jami’o’i a kasar nan, inda ya jaddada cewa kafa karin jami’o’i ya biyo bayan karuwar bukatar ilimi.

Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi ta tarayya mai ritaya, ya ce:

“Idan ana son magance matsalar, ku magance ta tun daga tushe”.

Ta hanyar dakatar da kafa sabbin cibiyoyi ne kawai saboda kuna son maida hankali kan jami’o’in da ake da su, alhali yana da kyau, kun manta da sauran matsalolin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke haifuwa kuma miliyoyin suna neman shiga da gurare kaɗan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.