INEC ta tsawaita rajistar katin zabe da makonni 2, zuwa karshen 31 ga watan Yuli.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya ranar 31 ga watan Yuli domin dakatar da gudanar da rijistar masu kada kuri’a da ake yi a fadin kasar nan, gabanin babban zabe na 2023.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai ya fitar, bayan wani taro na musamman da hukumar ta yi a Abuja ranar Juma’a.

Matakin a cewarsa shi ne baiwa hukumar damar aiwatar da sharuddan da ya kamata ta dauka kafin babban zaben kasar.

Ya bayyana cewa, domin tabbatar da cewa an yi wa ‘yan Najeriya rijista kafin ranar, an tsawaita sa’o’in yin rajistar zuwa sa’o’i takwas a kullum daga karfe 9 na safe zuwa 5 na yamma, ciki har da na karshen mako.

Okoye ya ce hukumar ta dauki matakin ne a taronta na ban mamaki inda ta tattauna da wasu abubuwa da suka hada da dakatar da aikin CVR da ke gudana.

Wannan ya biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a ranar Laraba 13 ga watan Yuli, 2022, inda ta yi watsi da karar da kungiyar kare hakkin dan adam da kuma tattalin arzikin kasa (SERAP) ta shigar na neman tsawaita aikin har zuwa ranar 30 ga Yuni, 2022.

Kotun ta tabbatar da cewa INEC na da ‘yancin sanya ranar da ta ga dama ta dakatar da CVR, muddin bai wuce kwanaki 90 kafin ranar da aka kayyade babban zaben ba kamar yadda aka tanadar a cikin Sec. 9(6) na Dokar Zabe 2022.

Okoye ya ce, bisa bin umarnin wucin gadi da kotun ta bayar, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan kararrakin, da kuma ba da dama ga ‘yan Nijeriya da dama su yi rajista, INEC ta ci gaba da yin CVR har zuwa ranar 30 ga watan Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *