Malamin musulunci, Sheikh Umar Maigona, ya rasu a kasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajji.

Allah ya yiwa shahararren malamin musulunci kuma mamba na hukumar jin dadin alhazai na jihar Gombe, Sheikh Abdulrahman Umar Maigona, rasuwa.

Shahararren malamin musulunci kuma mamba na hukumar jin dadin alhazai na jihar Gombe, Sheikh Abdulrahman Umar Maigona, ya rasu a Makkah, kasar Saudiyya. Maigona ya kwanta dama ne bayan kammala aikin hajjin 2022.

Marigayin wanda ya limamin masallacin na JIBWIS ne da ke No. 8, Gombe, ya koma ga Allah a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli, masaukin Namma Muwada, bayan yar gajeriyar rashin lafiya kamar yadda Muslim News Nigeria ta ruwaito.

Shugaban tawagar kiwon lafiya na hukumar aikin hajji ta kasa, Dr Usman Shu’aibu Galadima, wanda ya tabbatar da lamarin. Ya ce an shigo da Maigona da misalin karfe 1:00 na rana kuma nan take aka shiga kula da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *