Yajin aiki: Maimakon a magance matsalar Ngige ya shagaltu da zagin abokan aikin sa – Shugaban ASUU

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, a ranar Alhamis, ya caccaki ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, kan halinsa kan yajin aikin da malaman jami’o’in suka shiga.

“Ministan maimakon ya nemi yadda zai warware matsalar ya shagaltu da cin zarafin abokan aikinsa, yana cin zarafin har da Ministan Ilimi” inji shi da yake magana da sunrise daily.

Kalaman na Shugaban ASUU na nuna sabon ci gaba a rikicin da ya barke tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar kan yajin aikin da ta sa daliban jami’o’in a gida tun ranar 14 ga watan Fabrairu..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *