Shugabancin Musulmi da Kirista bai kai mu ko ina ba.

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya yi watsi da cece-kucen da ake yi kan zaben musulmi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu.

Oshiomhole ya ce lokaci ya yi da kasar nan za ta kawar da ra’ayoyin farko irin na addini da kabilanci, sannan ta mayar da hankali kan cancanta da jajircewar ‘yan takara don ceto kasar.

Da yake magana a gidan talabijin na TVC a ranar Alhamis, tsohon gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da tikitin jam’iyyar APC Musulmi da Musulmi, yayin da ya kuma yaba wa Tinubu kan yanke wannan shawarar.

Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.

Ya ce:

“Idan jam’iyyar adawa ta kara shiga muhawarar Musulmi da Musulmi, na gamsu da cewa shawarar Asiwaju Bola Tinubu ta yi daidai”.

“Mun yi gwagwarmaya don daidaita wannan al’amuran addini a cikin ‘yan shekarun nan. Matakin na Tinubu ya nuna cewa zai dauki kwakkwaran mataki idan aka zabe shi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.