Yadda muke siyan kaya da alat na bogi – Mutumin da ake zargi da damfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kama wani matashi dan shekara 45 mai suna Adewale Adesanya da laifin yin satar ta hanyar tura alat na banki na bogi domin damfarar ‘yan kasuwar Point of Sale (POS) da ‘yan kasuwa.

Adesanya, wanda aka kama shi da kwalabe guda hudu na giya shampain, Dom Perignom, wanda kowanne farashinsa ya kai Naira 117,900. ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa abokin aikinsa a wannan sana’ar ne ya horar da shi kan wannan damfara.

Ya ce sun sayi kayayyaki na miliyoyin naira ta hanyar amfani da alat na bogi da wasu aikace-aikace a wayarsu.

Wanda ake zargin ya ce ciniki na karshe da ya yi wanda ya fallasa shi kusan Naira 185,000 ne inda ya damfari wani ma’aikacin POS a Ibadan.

Ya ce, “Ba zan iya ci gaba ƙarya ba. Gaskiya muna yin damfara. Muna da aikace-aikacen waa da muke amfani da su don samar da faɗakarwar karya ga ma’aikatan POS.

Ba ni kadai nake yi ba. Mutum na biyu ya gudu lokacin da ya ji an kama ni. Muna samun miliyoyin naira da wannan sana’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *