‘Ya kamata gwamnati ta gagauta ta amince da biyan naira biliyan 200 ga ASUU domin kawo karshen yajin aikin’ – Falana

Dan rajin kare hakkin bil’adama kuma babban lauya, Femi Falana, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gabatar da karin kasafin kudin kasafi na naira biliyan 200 da ake bukata domin gyara jami’o’in gwamnatin tarayya a fadin kasar nan.

A cewar Mista Falana, hakan zai taimaka matuka wajen kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta yi na tsawon watanni da suka gabata wanda ya gurgunta jami’o’in gwamnati tun a watan Fabrairu.

Mista Falana ya ce koken da Shugaba Buhari ya yi kwanan nan kan yajin aikin da aka dade bai kamata ba.

Ya kuma caccaki gwamnatin tarayya na cewa ba ta da kudaden da za ta biya bukatun ASUU, inda ya ce gwamnati ta ware tiriliyan domin magance batutuwan da suka hada da tallafin man fetur da manufofin noma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *