Abdullahi Umar Ganduje, Nasir El-Rufai da Sauran Gwamnonin APC Sun Ziyarci Buhari A Daura, Sun Yabi Tikitin Tinubu-Shettima.

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Litinin sun yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarci gidansa da ke Daura.

Bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasar, gwamnonin sun ce sun gamsu da zabin Bola Ahmed Tinubu na Kassim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Gwamnonin da suka yi wannan ziyarar sun hada da Aminu Masari na Katsina, Abdullahi Ganduje na Kano, Nasir El-Rufai na Kaduna, Atiku Bagudu na Kebbi, Abubakar Bello na Neja, Hope Uzodimma na Imo, Kayode Fayemi na Ekiti, Simon Lalong na Plateau da Abdullahi Sule of Nasarawa.

Da yake jawabi bayan taron, Bagudu ya ce shugabancin Tinubu-Shettima zai karawa dukkan nasarorin da aka samu cikin shekaru bakwai da suka gabata karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bagudu ya ci gaba da bayyana cewa kungiyar gwamnonin APC na aiki tukuru domin ganin ta lashe zaben gwamnan jihar Osun da ke tafe.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana zabin Shettima a matsayin yanke shawara na gamayya.

Ya kuma yi nuni da cewa gwamnonin jam’iyyar APC 22 za su kai jihohi 22 a zaben 2023 mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.