Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta nemi afuwar maniyyata 1,809.

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta nemi afuwar maniyyata 1,809 da suka kasa gudanar da aikin hajjin da ake yi a halin yanzu da kuma hukumar alhazai ta jahohi da masu gudanar da yawon bude ido masu zaman kansu.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar hulda da jama’a, Hajiya Fatima Sanda Usara, hukumar ta ce.

“Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) cikin kaskantar da kai ta amince da wadannan abubuwa: cewa tana matukar nadamar dukkan maniyyata aikin hajjin 2022 kan wahalhalu da rashin jin dadin da aka samu a lokacin aikin jigilar jirage zuwa kasa mai tsarki”.

“Hukumar ta nemi afuwar gwamnatin tarayyar Najeriya, da hukumomin Alhazai na Jihohi, masu gudanar da balaguro masu zaman kansu, da sauran jama’a kan duk wani abin kunyar da lamarin ya faru a makonnin da suka gabata”.

“Abin takaicin shi ne, duk da kokarin da aka yi na jigilar dukkan maniyyatan Najeriya da ke son zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2022, NAHCON ta gaza wajen sauke wannan nauyi, musamman saboda koma bayan da aka samu a karshen makon da ya gabata, wanda ya kawo cikas ga shirinta na kammala jigilar maniyyatan zuwa ranar 27 ga watan Yuni na wannan shekara”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *