Gwamnatin Tambuwal ta rabawa marayun Sokoto N28.7m da shanu.

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce ta raba Naira miliyan 28 da digo 7 ga Hakimai 87 da shanu ga marayu a jihar, domin su samu damar gudanar da bukukuwan Sallah Eid-el-Kabir.

Malam Muhammad Maidoki, Shugaban Hukumar wanda ya sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan a wasu gundumomi a Sakkwato a ranar Asabar, ya ce kowane gundumomi 87 sun samu Naira 330,000.

Maidoki ya ce hakan na daga cikin kokarin gwamnati na tallafawa marayu da marasa galihu a jihar. Ya ce atisayen wani taron shekara-shekara ne da ake shiryawa domin karfafa gwiwar masu hannu da shuni wajen tallafawa marasa galihu daga cikin su.

Shugaban ya yabawa hakimai bisa sadaukarwar da suka yi wajen ganin an samu nasarar shirin. Maidoki ya kuma mika shanu uku a madadin Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ga ‘yan gudun hijirar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *