“Ba Za Ku Iya Sa Wike Ya Fice Daga PDP Ba” – Inji Bukola Saraki Ga Gwamnonin APC

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana ziyarar da wasu gwamnonin jam’iyyar APC suka kai wa takwaran su na jihar Ribas, Nyesom Wike, a matsayin aikin banza.

Gwamnonin jihohin Legas, Ekiti da Ondo, Babajide Sanwo-Olu, Dr Kayode Fayemi da Olurotimi Akeredolu sun gana da Wike a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas a ranar Juma’a.

Sai dai da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, bayan kammala bukukuwan Sallah, Saraki ya ce ziyarar ba ta da wani amfani “saboda PDP ba za ta bar Gwamna Wike ya tafi ba”.

“Gwamna Wike muhimmin dan jam’iyyarmu ne, kuma ina da yakinin cewa nan da wani lokaci mai nisa, za mu zauna mu magance dukkan matsalolin. Babu shakka cewa yana da dalilin jin yadda yake ji, amma akwai hanyoyi mafi kyau da za a iya magance irin wannan batu.

Abu mai kyau shi ne mu yi magana da juna. Muna kan halin da ake ciki kuma PDP za ta sake haduwa kuma ta yi gaba don samun nasara a zabe mai zuwa. Ina tabbatar muku da cewa tabbas PDP za ta warware matsalar danginta da take fama da ita a halin yanzu”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *