Mahajjata ‘Yan Najeriya Sama da 3,600 ba su samu tafiya ba.

Wannan dai shi ne babban aikin hajjin na farko da ke gudana tun bayan dambarwar da annobar cutar korona ta haifar a farkon shekarar 2020. A cikin 2020 da 2021, tsirarun mazauna Saudiyya ne kawai suka gudanar da hajji.

Wannan Shekarar, ‘yan kasashen waje 850,000 da ‘yan cikin gida 150,000 ne suka shirya gudanar da aikin hajjin.

Har yanzu adadin ya yi nisa da kusan miliyan biyu da rabi da suka yi aikin hajjin shekara ta 2019.

Sau biyu dai Najeriya ta samu karin wa’adin ne bayan ta kasa kammala jigilar maniyyata ta jirgin sama.

An ware wa kasar guraben aikin hajji 43,008. Amma har zuwa lokacin da aka rufe sararin samaniyar Saudiyya don neman mahajjata, An ta tattaro cewa akalla maniyyata 2,550 da suka biya ta hanyar hukumar aikin hajjin jihohi da kuma maniyyata 1,110 da suka dauki nauyin gudanar da balaguro masu lasisi ba za a iya jigilar su ba.

Wannan baya ga daruruwan wasu da suka kasa samun biza duk da biyan kudin tafiya. Wani na cikin hukumar ya shaida wa daya daga cikin ‘yan jaridarmu cewa an ba hukumar biza 33,936 ga maniyyatan da suka biya ta hukumomin jihohi daga cikin 31,386 aka dauke su ta jirgin sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published.