Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin 11 da Talata 12 ga watan Yuli 2022 a matsayin ranakun hutu domin gudunar da bukukuwan sallar Eid-el-Kabir na wannan shekara.

Ministan harkokin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar Dr Shuaib Belgore ya fitar a ranar Alhamis.

Ya taya daukacin al’ummar Musulmi da ‘yan Nijeriya na gida da na kasashen waje murnar wannan rana.

“Ina kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da koyi da ruhin soyayya, zaman lafiya, kyautatawa da sadaukarwa, kamar yadda Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi misali da su da kuma amfani da lokacin wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya, hadin kai, wadata da kwanciyar hankali. na kasar nan, duba da kalubalen rashin tsaro da muke fuskanta a halin yanzu,” Aregbesola ya kara da cewa.

Ministan harkokin gida Rauf Aregbesola

Ministan ya ba da tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta “dage wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya baki daya, tare da baiwa ‘yan kasa damar samun nasarar rayuwa, samar da tsare-tsare na zuba jari da samar da isasshen tsaro a makarantun.”

Aregbesola, yayin da yake yiwa Musulmai barka da Sallah Eid-el Kabir, ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauki nauyin kai karan duk wani mutum da ake zargi da aikata laifuka da suka gani a kusa da su ga jami’an tsaro tare da yin amfani da aikace-aikacen N-Alerts da aka tsara don magance matsalolin tsaro. .

Ya kuma umarci dukkan ‘yan Najeriya da su yi taka tsantsan da lura da masu kutsawa cikin al’ummarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *