Kungiyar Ansaru ta yi barazanar fara yi wa fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ke hannunta yankan rago.

A wani sauti da ya yi ta yawo a cikin dare kafin wayewar garin Laraba, an ji wasu da ake zargin ’yan kungiyar ne suna barazanar yi wa mutanen da ke hannunsu yankan rago saboda gwamnati ba ta nemi a sake su ba.

Mawallafin jarida kuma daya daga cikin masu shiga tsakani domin a sako fasinjojin, Tukur Mamu, ya tabbatar da sahihancin sautin, da cewa kungiyar na barazanar cewa ranar Laraba za ta fara yi wa mutanen yankan rago. 

A ranar 28 ga watan Afrilu ’yan bindiga suka kai harin bom kan wani jirgin kasa da yake hanyar zuwa Kaduna daga Abuja, suka kashe mutane kimanin 1o suka yi garkuwa da wasu sama da 50, ciki har da mata da kananan yara da wani dan kasar waje.

Daga bisani sun sako 13 daga cikin mutanen, amma suka ci gaba da rike sauran.

A makon jiya ne rahotanni suka bayyana cewa wani dan kungiyar ya harbi daya daga cikin fasinjojin da ke hannunsu, amma kungiyar ta ce ‘a bisa kuskure ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *