Fursunoni sama da 500 sun tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.

A ranar Talata, 5 ga watan Yuli ne wasu yan bindiga suka kai farmaki gidan gyara hali na Kuje da ke babban birnin Abuja.

Hakan ya biyo bayan farmakin da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka kai gidan gyara halin a daren ranar Talata, 5 ga watan Yuli.

An ruwaito cewa wata majiya ta gidan yari da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewar fiye da fursunoni 300 ne suka tsere a yayin harin yan bindigar.

Majiyar ta yi ikirarin cewa maharani sun yi amfani da bama-bamai wajen samun karfin iko a wuraren shiga da fita guda hudu.

Shashin BBC Pidgin ya rahoto cewa daya daga cikin jami’an ma’aikatar cikin gida ya ce rundunar tsaro sun daidaita lamarin, amma bai bayar da cikakken bayani ba. Hakazalika rahoton ya ce ana hasashen wasu adadi na fursunoni sun tsare daga cibiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *