Wani dan bindiga a kasar Amurka ya bude wa mutane wuta daga saman bene a inda suke gudanar da bikin ranar dimokuradiyar kasar.

Dan bindigar ya hau wani bene ne, inda ya rika harbin masu kallo da wata babbar bindiga.


Wannan dai shi ne harin na 180 da aka yi wa mutane Amurka a shekarar 2022 – ana samun daya a kowane mako a 2022. Shugaba Joe Biden ya ce ya kadu da tashin hankalin game da lamarin.

Sa’o’i kadan bayan haka, wasu ‘yan sanda biyu sun jikkata a wani harbi da aka yi a Philadelphia a ranar hudu ga watan Yuli.


Mutane biyar sun mutu a wurin da lamarin ya faru. Akalla mutane dozin biyu sun jikkata.


Daya daga cikin wadanda suka mutu mai suna Nicolas Toledo,mai shekaru 70 , wanda ya yake a wurin ne kawai saboda yana bukatar kulawa kuma danginsa ba sa son halartar taron.


Anand P, wanda yake wurin da lamarin ya faru ya ce:

“Mun je samun kyakkyawar rana ta iyali – sannan ba mu zata ba wannan harbin zai faru ba.”


“A tunani na, mota ce ta ci baya. Daga nan sai mutane suka fara gudu – don haka muka fara gudu.”

Ku Kalli Bidiyon:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *