An yi kira ga malaman addinin Islama da kada su shagaltu da tallafi da suke samu daga shugabannin siyasa.
Wani jami’a Farfesa Azeez Taofiq ne ya yi wannan kiran a wajen wani horo na yini daya ga malaman addini a Sakkwato.
A cewar Farfesa Taofeeq, cin hanci da rashawa ne ke haifar da duk wani sharri, ya kara da cewa rashin tsaro da aka samu a kasar ya samo asali ne sakamakon cin hanci da rashawa.
“Mun zo nan ne domin mu gaya wa Imaman mu da su yi amfani da harsunan su, su yi magana a kan fasadi. Kada su shagala da abin da suke samu daga ’yan siyasa. Su tattara su fada musu gaskiya.
“Saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya umarce mu da mu gyara abubuwan da ba daidai ba da hannun mu, idan za mu iya da harsunan mu, idan za mu iya sai mu kyamace ta a cikin zuciyarmu. ” in ji shi.
Shima da yake jawabi, Sarkin Alhabibiyya na kasa, Ustaz Adeyemi Fu’ad, ya bayyana cewa, an shirya wannan horon ne domin fadakar da mahalarta taron kan bukatar dogaro da kai da kuma fada da cin hanci da rashawa.