Yanzu muke samun labarin cewa, ALlah ya yiwa fitaccen daraktan masana’antar Kannywood, Nura Mustapha Waye.
A rahoton da muka samu daga kafar labarai ta DW ya ce, wasu makusanta sun ce an rabu da marigayin da daren jiya cikin koshin lafiya.
Za a yi jana’izarsa ne a makarantar Goren Dutse a jihar Kano
Babban jarumin gaba-gaba a shirin fim din na Izzar So a shafinsa na Instagram ya sanar da rasuwar daraktan a wani rubutu da ya yi. A cewarsa:
“Innalillahi wainnailaihirrajiun Allah Ya Karbi Rayuwar Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO Za Ayi Zanaidarshi Karfe 11 Na Safennan A Gidansa Goren Dutse Primary Insha Allah, Allah Ya Yafe Masa Kurakuransa Amin, Allah Yasa Idan Tamu Tazo Mu Cika Da Imani Amin.”