“Babban kalubalen daga tattaunawar da muka yi da jam’iyyar Labour Party shi ne wanda zai tsaya takarar shugaban kasa idan jam’iyyun suka yi maja”. – Rabiu Musa Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso, ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar NNPP, a ranar Asabar ya shawarci tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da ya amince da tayinsa na zama abokin tafiyarsa a zabe me karatowa.

A cewar jigon jam’iyyar NNPP, kudu basa da gogewa a fannin siyasa, ya kamata abokinsa Peter Obi ya amshi tayinsa na zama mataimakinsa saboda wannan ita ce babbar damar kudu.

Kwankwaso ya ce, idan Obi ya amince ya amshi tikitin takarar mataimakin shugaban kasar jam’iyyar NNPP a 2023, hakan zai bawa yankin Kudu maso gabas damar cika burinsu na mallakar mukamin shugaban kasa nan gaba.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa, amincewa ya zama abokin tafiyar da Obi ko wani daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa zai yi sanadiyyar durkushewar jam’iyyar sa, NNPP.

Kwankwaso, wanda ya je jihar Gombe don rantsar da sabbin ‘yan jam’iyyar da aka zaba, ya bayyana hakan ne a wata zantawa da manema labarai. A cewar, gogewarsa a harkar siyasa na tsawon shekaru da dumbin sanin aiki, ya taimaka ga abubuwa da dama a kasar, wanda hakan ne yasa NNPP ta samu karbuwa cikin kankanin lokaci.

“Daga tattaunawar da muka yi da jam’iyyar Labour, babban kalubale shi ne wanda zai tsaya takarar shugaban kasa idan jam’iyyun suka yi maja,” a cewar Kwankwaso.

“Daga karshe, wasu daga cikin wakilanmu sun kawo shawarar ya kamata a saka matakai kamarsu shekaru, matakin karatu, mukaman da aka taba rikewa a baya, kwazo da sauransu,” a cewar ‘dan takarar shugaban kasar NNPP.

“Tabbas dayan bangaren ba za su amince da haka ba. Da yawansu sun yi amanna da cewa ya kamata mulki ya koma can (Kudu maso gabas). “Na dauki tsawon shekaru 17 ina aikin gwamnati, muna maganar shekaru 17 na tsananin jajircewa, wanda hakan ne ya ke rike NNPP a yanzu,” a cewarsa.

Shugaban jam’iyyar NNPP ya ce ba yana kalubalentar mika mulki ga wani yankin kasar bane, amma dole a yi dubi da “matakai, lissafin siyasa da dabarbaru.” A cewarsa, Kudu maso gabas sun kware a harkar kasuwanci kuma suna da kwazo amma ya kamata su koyi siyasa.

“A siyasa an barsu a baya,” a cewar Kwankwaso. Ya ce yankin sun tsaida ‘dan takarar shugaban kasa da mataimakansu duk daga jam’iyyar APC da PDP amma yanzu suna da dama da NNPP.

Ya ce wadanda ke cewa “koda abokina (Peter Obi) na son amincewa ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, wasu daga cikin ‘yan kudu maso gabas ba za su amince ba, wannan ba dabara bace.” Kwankwaso ya ce wannan ita ce babbar dama ga kudu maso gabas da su yi maja da NNPP,

“wannan ita ce babbar dama da suke da ita, idan suka rasa, hakan zai zama annoba.” Game da wanda yake son ya zama abokin tafiyarsa, Kwankwaso

ya ce

“Muna da zabi a NNPP na daukar abokin tafiyar a kudu wanda yafi cancanta daya daga cikin wadanda nake magana shi ne Peter Obi.” Game da yiwuwar NNPP ta kai labari a zaben 2023, Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa na da tsari, fasali da yawan mabiya a fadin kasar da zasu iya takara gami da cin zabe.

Daga karshe, ya ce idan aka zabesa shugaban kasa a 2023, burinsa shi ne zai samar da wata kafa da matasan Najeriya zasu samu aiki, cika burinsu da karfafa a fannin ilimi da tattalin arzirki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *