Wani Lauya a Jihar Anambra Ya Je Kotu Da Kayan Fasto Kwanaki Bayan Wani Ya Je Kotu Da Kayan Bokaye.

Wani lauya, Ogbachalu Goshen, a ranar Alhamis ya bayyana a Kotun Majistare ta Okpoko a karamar hukumar Ogbaru kusa da Onitsha sanya da kayan raban fada.

Sai, dai an kawo karshen shari’ar a kotun cikin gaggawa, CB Mbaegbu, ya ki amincewa da shigar lauyan, ya kara da cewa ba zai yiwu ya zo kotu da wannan tufafin ya kare wani ba, The Punch ta ruwaito.

Goshen, a bangarensa, ya ki amincewa da alkalin kotun, ya ambaci hukuncin kotun koli da ta bawa dalibai mata damar saka hijabi a makarantun gwamnati.

Ya kuma ce yana da ikon yin hakan, yana mai cewa alkalin kotun ya danne masa hakkin da sashi na 38 na kundin tsarin mulki na 1999 na Najeriya ta bashi.

An kawo karshen zaman kotun bayan bangarorin biyu sun gaza cimma matsaya. Abin da Goshen ya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.