Baiwa Al’umma Damar Mallakar Bundigu Zai Iya Janyo Tabarbarewa Tsaro A Jihar – PDP Ta Zamfara Ta Gargadi Matawalle.

Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta yi adawa da umarnin Gwamna Bello Matawalle ga al’ummar jihar su mallaki makamai don kare kan su.

Sakataren jam’iyyar PDP a jihar, Faruku Ahmed, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce matakin barin jama’a su rike makami ka iya haifar da rudani da nuna kyama ga jam’iyyun adawa.

“A matsayinmu na ‘yan kasa masu son zaman lafiya kuma masu bin doka da oda, muna zargin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya kan mayar da irin wannan nauyi na tsarin mulki ga talakawa,” in ji shi.

“Wannan ya bayyana fili cewa hukumomin tsaro, kungiyoyi da masana shari’a a ciki da wajen jihar sun nuna adawa da sayen makamai.”

A cewar Ahmed nauyi ne ga gwamnatocin jihohi da na tarayya su kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Maimakon karfafa wa mazauna yankin gwiwa da su rike makamai, ya ce jam’iyyar ta shawarci gwamnatin jihar da ta dauki jami’an tsaron al’umma irin na JTF.

“Muna fatan za su kasance da kayan aiki da kyau, kuma za a biya su albashi,” in ji shi.

Ya kara da cewa shawarar ta kasance mafi kyawun zabi fiye da yanke shawarar “ambaton kayan aikin da za a cutar da ‘yan adawar siyasa a jihar”.

Jam’iyyar PDP ta dora alhakin rikicin mallakar bindiga a kan jam’iyyar All Progressives Congress, inda ta zargi jam’iyyar da bai wa gwamnan damar kai wa jam’iyyun adawa a jihar hari.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Rashin gazawar gwamnatin APC mai mulki ya sa Gwamna Bello Matawalle ba shi da wani zabi illa yin amfani da matsalar rashin tsaro a jihar wajen damfarar jam’iyyun adawa a jihar”.

“Saboda haka, PDP ta dauki wannan atisayen a matsayin wani yunkuri na karkatar da dukiyar jama’a”.

Jam’iyyar ta yi kira ga jami’an tsaro da su dakatar da Gwamna Matawalle daga “shirinsa mai hadari” na barin mutane su rike makamai.

“Muna kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, DSS da NSCDC da su sanya ido a kan mugun nufi na afkawa jam’iyyun adawa ta hanyar amfani da kwamitocin tsaro daban-daban da gwamnatin jihar Zamfara ta kafa saboda tsarin da ake bi yana da matukar wahala.” jam’iyyar ta ce.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Lahadin makon da ya gabata ya umurci al’ummar jihar da su shirya tare da samun lasisin rike bindigogi domin kare kansu daga ‘yan ta’adda a jihar.

Matakin dai ya janyo cece-kuce kuma babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, Janar Lucky Irabor ya caccaki shi.

“Ba na tunanin cewa gwamna yana da ikon umurci kwamishinan ‘yan sanda ya ba da lasisi, saboda kwamishinan ‘yan sanda ba shi da hurumin bayar da lasisi,”

in ji Janar Irabor a yayin bude taron hadin gwiwa na kasa da kasa. Kwalejin tsaro da kwalejojin yaki na sojojin Najeriya da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *