Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jadada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta yi zabe na adalci kuma cikin zaman lafiya a 2023.
Ya bada tabbacin cewa ba zai yi wa INEC katsalandan ba, yana mai cewa bayan kammala zaben cikin gida na jam’iyyu, yanzu an sa ido ne kan zaben 2023 a Najeriya.
Buhari, a cewar sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter, ya yi magana ne a daren ranar Laraba a Lisbon yayin ganawarsa da yan Najeriya da ke zaune a Portugal.
“Muna fatan ganin an mika mulki ga gwamnati na gaba ba tare da tangarda ba. Kamar yada na fada a baya ba za mu yi kasa a gwiwa wurin yin abin da ya dace ba don walwalar yan Najeriya na gida da waje,” in ji shi.