Hukumar ICPC ta yi karar Edike Mboutidem Akpan, mataimakin kwamanda a hukumar NSCDC a kotu kan zargin damfara ta N26.6m.

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta yi karar wani mataimakin kwamanda na hukumar tsaro ta NSCDC, Edike Mboutidem Akpan a wata babban kotun tarayya a Abuja kan zarginsa da amfani da kamfanin dillancin gidaje/filaye, Danemy Nig Ltd, don damfarar kwastomomi kudi har N26,655,000.

Mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ogugua ya ce an gurfanar da wanda ake zargin a gaban Mai sharia V.S. Garba kan tuhuma guda 17.

Ta ce takardar gurfanarwar ta nuna cewa Akpan ya yaudari masu sayan fili da dama ta hanyar ikirarin hadin gwiwa da NSCDC suka biya kudade daban-daban don siyan filaye a Karshi, Jihar Nasarawa da Sabon Lugbe Extension, Abuja, kuma ba a basu filayen ba. Wani bangare na sanarwar ta ce:

“A daya cikin tuhumar, Ana zargin Mr Akpan ya karbi N13,350,000 a shekarar 2011 daga wani Mr Igwe Onus Nwanko, ta kamfaninsa, Danemy Nig Ltd, don sayar masa filaye 10 a Airport Road.

“A kuma zargin ya karbi N1,305,000 a lokuta da dama daga hannun Dr Robert Okoro da Akuneme Marcel Ikwuoma, don basu filaye a Defenders Family Estate, Airport Road.

“An kuma zargi jami’in na NSCDC da karbar N2,610,000 daga Mrs Chidinma Obasi na filaye biyu da N1,205,000 daga Mr Etuchere Martins don fili.”

Dangi da ‘yan uwa na saka ‘yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari A wani rahoton, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, yace matsin lamba da yan uwa da abokanai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar Jarida The Sun, Mr Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin ‘Corruption Tori Season 2’ da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.