Farashin kuɗin tafiya a jirgin sama zuwa wasu biranen arewa sun tashi yayin da mutane suka fara komawa gida gabanin babbar Sallah.

Yayin da al’ummar Musulmai a Najeriya ke shirin shagulgulan babbar Sallah nan da mako ɗaya, farashin tafiya a jiragen sama ya ƙaru a wasu manyan hanyoyi a faɗin Najeriya. Kamfanonin jiragen sama na cigaba da alaƙanta alhakin ƙaruwar kuɗin tikitin kan tashin kuɗin litar Man Jirgin wanda ake kira da ‘Jet A1’.

Mafi yawan hanyoyin da lamarin ya shafa na arewa ne kamar yadda binciken maneman labarai ya nuna cewa, kuɗin tafiya a jirgin sama zuwa manyan biranen arewa ya tashi duk da kukan da Fasinjoji ke yi game da hakan.

Alal misal, Jirgin Legas zuwa Kano na mafi yawan kamfanoni da suka haɗa da, Air Peace, Azman Air da Max Air, suna karɓan N108,000 kuɗin tikitin zuwa kaɗai.

Idan muka duba Kamfanin jiragen sama na Air Peace, tikitinsa na Legas zuwa Kano ya kai N105,000 inda ya ƙaru kan yadda aka siyar makonni kalilan da suka shuɗe N70,000.

Hakanan kuma tikitin jirgin Air Peance na Legas zuwa birnin Ilorin ya kai N70,000 fiye da N50,000 da suka sanya a shafinsu na yanar Gizo-Gizo. Tafiyar da ta fi kowace tsada yanzu a Jirgin sama ita ce Legas zuwa Yola a jirgin Max Air, wanda tikitin ya kai N135,000, yayin da Lagos-Sokoto ke laƙume N128,000 kuɗin zuwa kaɗai.

Har wa yau a kamfanin Max Air, Abuja-Katsina na cin N75,000, yayin da kuɗin jirgin Abuja-Kano ke tsakanin N65,000 zuwa N75,000. A ɗaya ɓangaren kuma Lagos-Maiduguri ya kai N105,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *