Babban dan Shugaban kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Shugaban kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya yi rashin babban dan sa, Isah Ango Abdullahi bayan gajeruwar rashin lafiya.

Wata majiya mai tushe wacce ta tabbatar wa wakilinmu a Zaria rasuwar, ta ce Isah ya rasu ne a ranar Alhamis da yamma a Abuja, inda ya ce za a kawo gawarsa Zaria a yau domin yin sallar jana’iza.

Majiyar ta bayyana cewa, za a gudanar da sallar ne a masallacin Juma’a na Haruna Danja da misalin karfe 1:30 na rana.

Har zuwa rasuwarsa Isa ma’aikaci ne a hukumar leken asiri ta Najeriya NIA a Abuja.

Ya bar mata da ‘ya’ya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.