Iyalan fasinjojin da aka yi garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun bukaci gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen ganin an saki wadanda aka yi garkuwa dasu bayan samun rahoto yadda aka harbi daya daga cikinsu.
Iyalan sun ziyarci wasu ‘yan majalisar tarayya a ranar Laraba, inda suka bukaci gwamnati da ta taimaka wajen nemo wadanda aka sacen.
Bamidele Salam ‘dan jam’iyyar PDP na jihar Osun, Mansur Sora, APC daga Bauchi da sauran guda 10 a makon da ya gabata sun kawo batun a majalisar, inda suka yi kira ga sakin wadanda aka yi garkuwa dasu.
Mai magana a madadin iyalan, matar wani wanda aka yi garkuwa da shi, Matilda Kabir, ta ce rashin tabbacin shi ne kisa.
A cewarta ba su san waye wanda cikin wadanda aka yi garkuwa dasu za a sake hara ba. Matar Kabir ta ce tsawon kwanaki 94, iyalan sun kasance cikin dari-dari ba tare da sanin makomar masoyansu ba.
“Labarin da muka samu a safiyar yau shi ne yadda aka bindige daya daga cikinsu. Mijina yana wurin. Bamu san wa za a sake hara ba. ‘Yan Najeriya su taimaka. Mijina yana can tsare,” tace.
Aminu Usman, wanda aka yi garkuwa da ‘dan uwansa ya bukaci ‘yan majalisa da su taimaka wajen hurawa gwamnati wuta wajen ceto wadanda aka yi garkuwa dasu.
Mr Bamidele ya ce majalisar na shirya hukumomin da suka dace kan lamarin. Ya tabbatarwa iyalan cewa gwamanati za ta yi iya kokarinta don ceto rayukan wadanda aka yi garkuwa dasu.
“Yayin da muke magana da gwamnati, muna cigaba da magana da masu sasanci – wadanda ke magana da masu garkuwa da mutane sannan muna sa rai da izinin Ubangiji za mu iya tabuka wani abu cikin kankanin lokaci,” a cewarsa.