Ekweremadu Ya Gurfana Gaban Kotu A Birtaniya Kan Zargin Cire Koda.

A ranar Alhamis ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya gurfana a gaban kotun majistare da ke Uxbridge a kasar Birtaniya kan tuhumar da ake yi masa na cire kodan wani yaro.


Mai gabatar da kara ya yi ikirarin cewa David Ukpo, wanda ya yi zargin cewa an tilasta masa bayar da kodar sa ga diyar Sanatan, ya cika shekara 15.


An dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 7 ga watan Yuli a Kotun Majistare ta Westminster don baiwa babban mai shigar da kara na Burtaniya, Suella Braverman damar sanin ko za a yi shari’ar a kasar ko kuma Najeriya.


A ranar Laraba ne majalisar dattawan ta ce ta aike da tawaga domin su ziyarci Ekweremadu da matarsa.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya bayyana haka ne bayan wani zaman sirri da ‘yan majalisar suka yi a Abuja.

Ya ce mambobin kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kasashen waje za su tafi Birtaniya nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.