‘Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun harba daya daga cikin fasinjojinj dake hannun su.

‘Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jrigin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris sun harba daya daga cikin fasinjojin da suka yi garkuwa da su.

Kamar yadda Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald wanda shi ke jagorantar sasanci da ‘yan ta’addan yace, wanda suka harban mai suna Mohammed Al-Amin yana cikin mawuyacin hali.

Mamu, wanda ya jagoranci sakin fasinjoji 11 daga cikin wadanda aka sace, ya tabbatar da wannan cigaban ga jaridar Daily Trust.

“Zan iya tabbatar muku cewa an harbi fasinja daya daga cikin wadanda aka sace kuma bayanin daga majiya mai karfi ne. Zai yuwu da gangan ne saboda su aiko da sako. Kashe wadanda suka sace abu ne da muka san zasu iya. SUn yi barazanar yin hakan tuntuni,” yace.

Yace gwamnati dole ne ta shirya daukar alhaki idan aka ki daukan mataki a kan lokaci.

Mamu yace akwai yadda suke samun bayanai amma har yanzu gwamnati ta ki daukan matak a kai.

“Na san irin rikicin dake tattare da wannan lamarin, hakan yasa nake ta jaddada cewa dole ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya daukar wasu matakai da doka bata aminta da su ba idan yana son ceto rayukan jama’ar nan,”

“A kan nasarar da muka samu, mun bude wata dama ne wacce gwamnati daga nan take da karfin kawo karshen lamarin cikin kwanaki uku zuwa hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *