Shugaban Majalisa, Ahmad Lawan, a ranar Laraba ya bayyana cewa ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya ta dauki hayan lauyoyi da za su kare Sanata Ike Ekweremadu da matarsa da a yanzu ke tsare kan zargin cire sassan jikin mutum.
Mr Lawan, ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin da ya ke bada bayani kan taron sirri da aka yi kafin fara zaman majalisar na ranar.
A cewar Lawan, wata tawaga daga kwamitinta na harkokin kasashen waje za ta bar Najeriya zuwa Landan a ranar 1 ga watan Yulin 2022, don ziyartar sanatan, rahoton Daily Nigerian. Lawan ya kara da cewa sun yanke shawarar saka baki kan halin da Ekweremadu ke ciki ne bayan sun tattauna da ofishin jakadancin Najeriya a Landan. Ya kara da cewa majalisar za ta tuntubi Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje da Ofishin Jakadancin Najeriya a Landan kan kama Sanata Ike Ekweremadu da yan sandan Birtaniya suka yi.
Ya ce:
“Na tattauna da jakadan mu a Birtaniya, Alhaji Isola Sarafa, wanda ya tuntubi takwararmu, wanda ya tura tawagarsa kotun Uxbridge inda aka kai Ekweremadu.
“Ofishin jakadancin ta dauki wasu lauyoyi da za su kare takwararmu. “Mun yaba musu kan matakin da suka dauka. An tuntubi Ministan Harkokin Kasashen Waje, don ma’aikatar ta bada tallafi ga takwararmu.”
Lawan ya kuma ce saboda batun na kotu ba za su iya daukan matakin da ya fi hakan ba a yanzu amma ya ce za su cigaba da hadin gwiwa da ofishin jakadancin don tabbatar da ganin an yi adalci.