Babban kotun tarayya a Abuja ta ki amincewa da batun sakin Nnamdi Kanu bisa beli.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar neman belin shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, Channels Tv ta ruwaito.

Mai shari’a Binta Nyako, a hukuncin da ta yanke a ranar Talata, ta ce batun cin zarafi ne ga tsarin kotun da kuma yunkurin kawo cikas ga ci gaba da shari’a kan batutuwan da ke gaban kotun.

Sai dai ta shawarci wanda ya shigar da kara ya tunkari kotun daukaka kara kan batun belin, idan bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba.

Alkalin kotun ya bayyana cewa tun daga lokacin da aka yanke hukunci a Yulin 2017 ta belin Kanu ya zuwa yau, an dage karar har sau 15 kuma har yanzu ba a ci gaba da sauraren karar ba.

Ta kara da cewa ba ta gamsu da dalilin da shugaban kungiyar ta IPOB ya bayar na rashin gurfana a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar sa ba, Punch ta ruwaito.

Mai shari’a Nyako ta bayyana cewa daga bayanan kotun, Kanu ya samu wakilcin lauyansa a ranar da aka soke belinsa, haka kuma wadanda za su tsaya masa, kuma ba a taba kin sauraransa ba ko yi masa adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *