‘Yan bindiga sun sake sace wani DPO a kan hanyarsa ta kama aiki a Kaduna.

‘Yan bindiga sun sace sabon DPO a kan hanyarsa ta kama aiki a Kaduna.

An yi garkuwa da wani sabon jami’in ‘yan sanda (DPO) da aka tura zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

An sace DPO din ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safe a ranar Litinin. Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa, DPO din na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kama aikinsa lokacin da aka sace shi.

Ba a bayyana ko jami’in na tafiya shi kadai a cikin motarsa ba ko tare da wasu ba lokacin da aka yi awon gaba da shi. Har yanzu dai ‘yan sanda ba su mayar da martani ko kuma fitar da wata sanarwa a hukumance kan sace jami’in ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *